Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya ACF, ta bayyana wasu tsare-tsare kan arewa ga masu neman takarar shugaban kasa a zaɓen 2027.
ACF mai fafutukar kare muradun yankin arewaci ta ce ba za ta fito fili ta nuna goyon baya ga wani ɗantakarar shugaban ƙasa daya ba a zaben 2027, kamar yadda Farfesa Tukur Muhammad-Baba sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar ya shaida wa BBC.
Sai dai ya ce za su diba kuɗurorin ƴantakarar da manufofinsu da kuma alƙawuran da suka ɗauka.
Ya ƙara da cewa nan da watanni masu zuwa ACF za ta gana da masu neman tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar ɗaya bayan ɗaya, don ta tantance manufofi da tanade-tanaden da kowannesu ya yi wa yankin na arewa idan ya ci zabe.
Ya ce zaman da za su yi da ɗantakarar zai tantance shirin da za su yi wa arewa da ma Najeriya baki ɗaya.