Home NewsMummanar gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar Litinin din da ta gabata.

Mummanar gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar Litinin din da ta gabata.

Mummanar gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar Litinin din da ta gabata.

 

Shugaban ƙungiyar kanikawa ta Sokoto Shehu Muhammad Raba ya bayyana cewa aƙalla shaguna 80 ne su ka ƙone baya ga lafiyayyun motoci biyu da aka tabbatar da ƙonewarsu.

 

Kasuwar wadda aka fi saninta da Buzaye Garage, ta shahara wajen samun abokan cinikayya da dama, cikinsu har da ƴan asalin maƙobciyar kasar nan wato Jamhuriyar Nijar.

 

Rahotanni sun bayyana cewa, gobarar ta samo asali ne sakamakon matsalar lantarki da aka samu a wani shagu da ke cikin kasuwar.

 

Gobarar ta shafe tsawon sao’i tana ci, kafin daga bisani jami’an kashe gobara na tarayya da na jiha su ka samu nasarar kashe ta, inda a halin yanzu ake tattara jimillar asarar da aka tafka.

You may also like

Leave a Comment