Home NewsDakarun sojin Najeriya ta ofureshan Whirl Stroke sun kai wani gagarumin farmaki wanda ya tarwatsa gungun ‘yan ta’adda da ke gudanar da munanan ayyukansu a tsakanin jihohin Benuwai da Taraba.

Dakarun sojin Najeriya ta ofureshan Whirl Stroke sun kai wani gagarumin farmaki wanda ya tarwatsa gungun ‘yan ta’adda da ke gudanar da munanan ayyukansu a tsakanin jihohin Benuwai da Taraba.

Dakarun sojin Najeriya ta ofureshan Whirl Stroke sun kai wani gagarumin farmaki wanda ya tarwatsa gungun ‘yan ta’adda da ke gudanar da munanan ayyukansu a tsakanin jihohin Benuwai da Taraba.

Kuma rundunar ta samu nasarar ƙwato wasu tarin bindigu da alburusai da gurneti a ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba.

Muƙaddashin mai magana da yawun haɗaɗɗiyar rundunar sojin, Ahmad Zubairu, ya ce, dakarun sojin sun kai samamen ne a ranar Lahadi bayan sun samu masaniyar zirga-zirgar wani ƙasurgumin shugaban gungun ‘yan ta’addan mai suna John Ngata.

Ya ce, sojojin sun yi gaggawar saka shinge a kan hanyar Zaki-Biam da ke jihar Benuwai inda ake zargin tanan ne za su wuce. A nan suka yi nasarar yi masa ƙofar rago.

“Biyo bayan tambayoyi, ‘yan bindigar sun yi kai sojoji inda suke ɓoye makamansu a ƙauyen Amadu da ke ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba,” In ji Zubairu.

Ya kuma ce dakarun sun ƙwato bindigu 13 samfurin AK-47 da kwanson alburusan AK-47 39 da alburusai na musamman guda 690 masu nauyin milimita 7.62 da gurneti guda 4 daga maɓoyar.

Sojojin sun lalata wurin ɓoye makamai domin magance amfani da wurin bayan dakarun sun kwashe makaman zuwa sansaninsu.

Kwamandan rundunar ofureshan Whirl Stroke, Moses Gara, ya ce, samun bayanan sirri ne suka taimaka wa rundunar wajen samun nasarar farmakin da suka kai da taimakon al’ummar yankunan.

Ya ce, wannan nasarar ta ƙwace makaman zai kawo ƙarshen yaɗuwar makamai masu haɗari a tsakanin ‘yan ta’adda.

Mista Gara ya bai wa sojojin tabbacin fifita walwalarsu da samar musu da kayan aiki domin zaman cikin shiri a kodayaushe a yayin da yake kira ga al’umma da su ci-gaba da samar da sahihan bayanan sirri ga rundunar.

Ya yi alƙawarin kiyaye bayanan dukkan waɗanda suka ba da bayanan sirrin.

Farmaki na baya-bayan da rundunar ta kai ya faru ne a iyakokin Benuwai da Taraba inda ‘yan bindigar ke amfani da shi wajen kai wa al’umma hare-hare da zama hanyar zirga-zirgarsu.

A ranar 11 ga watan Disambar 2025, dakarun rundunar ofureshan Whirl Stroke da ke aiki da dakarun ‘yan sanda Najeriya da dakarun tsaron jihar Benuwai, sun yi nasarar tarwatsa wasu gungun ‘yan ta’adda bayan tare musu hanya a mahaɗar Ukum da ke ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benuwai.

A yayin farmakin da ta kai watan Disambar 2025, an kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su uku waɗanda ake zargi da yi wa matafiya kwantan-ɓauna da yi wa musu fashi a kan hanyar da ta haɗa ƙauyukan Aturuku da Wembe da Ayati.

Majiyoyi daga cikin jami’an tsaro sun alaƙanta ƙungiyar wasu ‘yan bindiga da ke garkuwa da mutane da kewayen kasuwar doya ta Zaki-Biam a yankin Shitile ta ƙaramar hukumar Katsina-Ala.

Shugabanni a rundunar sojin Najeriya sun ce gano makamai da aka yi a watan Janairu a jihar Taraba na da nasaba ne da irin ɗambar da rundunar ta sa a gaba na tarwatsa gungun masu aikata laifi a jihohin Benuwai da Taraba, jihohin da suka sha fama da ayyukan masu garkuwa da mutane da fashi da makami da rikicin a tsakanin ƙabilu.

You may also like

Leave a Comment