Home NewsSanata Kwankwaso ya taya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Sanata Kwankwaso ya taya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Sanata Kwankwaso ya taya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Rabi’u Kwankwaso ya ya wallafa a shafin sa na Facebook.

A wannan rana, ina mika sakon taya murna da fatan alheri ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa zagayowar ranar haihuwarsa.

Ina waiwaye tare da godiya ga tsawon shekarun tafiyarmu ta siyasa tare, inda ya yi aiki a muhimman mukamai daban-daban—da fari a matsayin Mataimakina na Kaina (Personal Assistant) a zangona na farko da na yi a matsayin Minista, sannan ya zama Babban Mataimakin Sirri (Principal Private Assistant), daga bisani kuma Kwamishina a zangona na biyu. Yanzu kuma Allah Ya kaddara masa zama Gwamnan Jihar Kano, inda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen aiwatar da hangen nesa da shirye-shiryen da muka assasa domin cigaban Jihar Kano.

Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ƙara masa hikima, lafiyar jiki da ta zuciya, tare da nutsuwa da tsarkin niyya a wannan sabon shekarar rayuwarsa.

You may also like

Leave a Comment