Trump yayi barazanar ɗaukar mataki irin na Venezuela akan Colombia
Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soja kan gwamnatin Colombia, yana mai cewa matƙar Colombia bata yi abinda ya kamata ba, ba shakka akwai yiwuwar shugabanta ya shiga hannun Amurka.
Wallafawa ranar: 05/01/2026 – 16:24
Da yake bayani Trump ya ce ba shakka abinda Amurka tayi a Venezuela yayi masa daɗi, don haka akwai yiwuwar ya faɗaɗa aikin zuwa Colombia lamarin da ya haifar da martani mai zafi daga Bogota babban birnin ƙasar.
Trump ya yi waɗannan kalamai ne bayan Amurka ta kama Shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, a wani farmaki da aka kai da sassafe ranar Asabar, sannan aka kai shi New York domin fuskantar tuhumar safarar miyagun ƙwayoyi.
Yayin da yake magana da manema labarai, Trump ya zargi Shugaban Colombia, Gustavo Petro, da cewa ƙasarsa na fama da mummunar matsala, yana kuma zargin shi da kasancewa jagoran wata tawagar masu safarar hodar iblis da sayarwa a Amurka.
A martaninta, Colombia ta yi watsi da kalaman Trump, tana kiran su a matsayin barazana da ba za a amince da ita ba ga zababben shugaban ƙasa.
Ma’aikatar harkokin wajen Colombia ta bayyana cewa kalaman suna nuna tsoma baki kai tsaye cikin harkokin cikin gida na ƙasar, tare da saɓa wa ƙa’idojin dokokin ƙasa da ƙasa.