Home NewsGwamnatocin ƙasashen Tarayyar Turai sun amince su ci gaba da riƙe ko dakatar da kadarorin Rasha na sama da dala miliyan dubu biyu, da suka dakatar da gudanarsu a yankin ƙasashen na -EU, tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.

Gwamnatocin ƙasashen Tarayyar Turai sun amince su ci gaba da riƙe ko dakatar da kadarorin Rasha na sama da dala miliyan dubu biyu, da suka dakatar da gudanarsu a yankin ƙasashen na -EU, tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.

Gwamnatocin ƙasashen Tarayyar Turai sun
amince su ci gaba da riƙe ko dakatar da
kadarorin Rasha na sama da dala miliyan
dubu biyu, da suka dakatar da gudanarsu a
yankin ƙasashen na -EU, tun bayan da
Rasha ta mamaye Ukraine.

An riƙe yawancin kuɗin gwamnatin Rashar
ne a bankin Euroclear na Belgium.

Shugabannin Turai na sa ran cimma wata
yarjejeniya a mako mai zuwa – wadda a
ƙarƙashinta za a yi amfani da kuɗin a bayar
da bashin taimaka wa gwamnatin Ukraine.

Ukraine na fuskantar matsalar rashin kuɗi
ne bayan kusan shekara huɗu ana yaƙi, a
don haka ƙasashen Turai ke son taimaka
mata a matsayin ƙawarsu.

A kan wannan kudiri jami’an Rasha sun
zargi kungiyar ta Turai da sata.

A ranar juma’ar da ta gabata ne babban
bankin Rasha ya ce zai shigar da bankin na
Belgium -Euroclear ƙara a wata kotu a
Moscow – saboda shirin bayar da bashin
kuɗin.

You may also like

Leave a Comment