Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wata
ganawar sirri da gwamnonin jahohin Benue da
Kaduna da kuma Cross River a Fadar shugaban
Kasa da ke Abuja adaidai lokacin da ake fama da
Kalubalen tsaro da na Jagoranci awasu daga
cikin sassan Kasar nan.
Gwamnonin da su ka hadar da gwamna Hycinth
Alia na jahar Benue da Uba Sani na jahar
Kaduna da kuma Gwamna Bassey Otu na jahar
Cross River sun isa fadar shugaban Kasa ne a
lokuta mabanbanta kafin daga bisani su hadu su
rankaya su gana da shugaban kasa a Ofishinsa
da ke a kasan benen fadar shugaban kasa da ke
Abuja.
Sai dai duk da yadda ba a bayyana batutuwan da
su ka tattauna akai ba amma dai wata majiya mai
tushe ta ce tattaunawar ba ta rasa nasaba da
tsaro da kuma batun da ya shafi Jagoranci da ke
tunkarar jahohin uku da su ka hadar da fadace-
fadacen Kabilanci da matsalar ‘Yan bindiga da
kuma matsin tattalin arziki.
Bayan kammala taron gwamnonin ba su amince
sun tattauna da ‘Yan Jaridu ba inda bayan sun yi
bankwana da Juna sai kowa daga cikinsu ya
shiga motarsa wadda dama shi ta ke jira.
Kawo yanzu ita ma fadar shugaban kasa ba ta
fitar da wata sanarwa a hukunance akan dalilan
taron da gwamnonin ba.