Hukumar Kula da Taimakekeniyar lafiya ta Jahar
Kano ta ce ta sami Bunkasa a fannin inshorar
kiwon lafiya daga kulawa da mutane dubu Dari
hudu da Casa’in da Bakwai da Dari Biyu da Sittin
da Biyu a shekarar 2023 izuwa mutane dubu dari
tara da talatin da uku da goma sha hudu a
shekarar 2025.
Babbar Sakatariyar hukumar Dr Rahila Mukhtar
ta bayyana hakan ayayin Bikin kulawa da Koshin
lafiya na shekarar 2025 da ya gudana a nan
Kano.
A cewarta nasarar ta bayyana Kokarin gwamnati
na ba da kulawa ga Koshin lafiya ga al’ummar
Jahar Kano ta karkashin tsarin taimakekeniyar
lafiya.
Dr Rahila Mukhtar ta ce an kafa hukumar kula da
tsarin taimakekeniyar lafiya ta jahar Kano a
shekarar 2016 a karkashin doka mai lamba uku
domin bayar da tsarin samar da kudaden kulawa
da koshin lafiya ta hanyar tattara kudaden haraji
da kuma kyaututtuka domin kulawa da Koshin
lafiyar mazauna Jahar kano.