Home NewsRundunar Sojojin Najeriya mai yaki da matsalolin tsaro ta ce ‘yan bindiga,da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka ba za su samu sukunin aikata laifuka a shekarar 2026 ba.

Rundunar Sojojin Najeriya mai yaki da matsalolin tsaro ta ce ‘yan bindiga,da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka ba za su samu sukunin aikata laifuka a shekarar 2026 ba.

Rundunar ta kuma ce an tsauraran matakan tsaro domin kare babban birnin tarayya Abuja da kewaye.

Kwamandan rundunar ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce an ƙara tsaurara horaswa,da sintiri da ayyukan leƙen asiri, tare da zurfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin dakile duk wani yunƙuri na tada zaune tsaye.

Ya ce duk da cewa babban aikin rundunar shi ne kare yan kasa da manyan muhimman gine-ginen gwamnati,da rundunar ta faɗaɗa ayyukanta wajen yaki da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu laifi a sassan Abuja da jihohin makwabta.

Kwamandan ya bayyana cewa a shekarar da ke ƙarewa, rundunar ta samu nasarori da dama, ciki har da kama masu laifi, kwato makamai da tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda, lamarin da ya taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali a wasu yankuna.

Ya yi gargaɗi mai tsauri ga masu aikata laifuka da ke neman amfani da Abuja a matsayin mafaka, yana mai cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in barazana ga tsaro ba.

You may also like

Leave a Comment