NEMA
Hukumar ba da Agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce ta kammala daukar matakai a fadin kasar nan domin tabbatar da cewa an gudanar da bukukuwan karshen shekara cikin kwanciyar hankali.
Shugabar hukumar NEMA Zubaida Umar ce ta bayyana hakan a birnin tarayya Abuja ayayin da ta jagoranci ma’aikatan hukumar zuwa tattakin motsa jiki inda har ta bukaci ‘Yan Nigeria da su kasance cikin kulawa da koshin lafiyarsu har zuwa karshen bukukuwan na karshen shekarar 2025.
A cewarta hukumar NEMA ta kammala tsara tawagar kai daukin gaggawa wadda ta ke aiki da gwamnatin tarayya da matakin jahohi da kuma Kananan hukumomi domin rage radadin Afkuwar kowanne irin Ibtila’i.
Daraktan Sashen hulda da Jama’a na Hukumar Ba da Agajin gaggawa ta Kasa NEMA Manzo Ezekiel ya ce gangamin motsa jikin da shugabar hukumar ta jagoranta sun hadar da tattaki na tsahon kilomita 5 wanda ke da manufar farfado da kuzarin ma’aikatan hukumar tare da yin aiki tare, kamar yadda sharuddan hukumar NEMA su ka tanada.