243
Ƴan bindiga sun kai sabon hari garin Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a jihar Kano, inda suka sace mutum bakwai.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne a daren jiya Lahadi a ƙauyen Zurin Mahauta da ke yankin.
Wakilinmu, Sufyan Halilu Getso, ya tattauna da mai unguwar Zurin Muhauta, Murtala Mai Unguwa, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya ce jami’an tsaro sun dauki mataki cikin gaggawa tare bin sawun masu garkuwa da mutanen.