Shugaban Rundunar, Kayode Adeolu Egbetokun, ya sanar da haka tare da jaddada cewa babu wata kotu da ta hana aiwatar da tsarin, wanda za a fara ne daga ranar 2 ga Janairu, 2026.
Ya ce Hukumar ta yanke wannan shawara ne bayan ta lura da sabbin matsalolin tsaro da kuma buƙatar kare rayukan ’yan Najeriya.
Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya ce an samu mummunan ƙaruwar laifuka ta hanyar amfani da motoci masu gilashi mai duhu ba tare da izini ba.
Ya ce, “Rundunar ’Yan Sandan Najeriya na sanar da jama’a cewa za a ci gaba da aiwatar da dokar izinin gilashi mai duhu yayin da ake jiran hukuncin karshe na shari’ar da ke gaban kotu.
“Wannan mataki ya biyo bayan nazari mai zurfi kan sabbin matsalolin tsaro da kuma bukatar kare rayukan ’yan ƙasa.
“Ya kamata a fayyace cewa babu lokacin da wata kotu ta hana Rundunar ’Yan Sandan Najeriya aiwatar da dokar da ta shafi amfani da gilashi mai duhu a kan motocin.
“Duk da haka, Rundunar ta dakatar da aiwatar da dokar na ɗan lokaci domin ba wa direbobi damar hada takardunsu da kammala rajista ba tare da matsin lamba ba.”
“Wasu mutane da kungiyoyin aikata laifuka sun yi amfani da wannan gibi wajen boye kansu da kuma sauƙaƙa aikata laifuka daga fashi da makami zuwa garkuwa da mutane da sauran laifukan tashin hankali.
“Saboda haka, Rundunar ta ga ya zama dole kuma gaggawa ta ci gaba da cikakken aiwatar da dokar a matsayin matakin kariya ga al’ummominmu.
“Saboda haka, aiwatar da izinin gilashi mai duhu zai ci gaba daga 2 ga Janairu, 2026.
“Babban Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ya tabbatar wa jama’a cewa aiwatar da dokar zai gudana cikin kwarewa, girmama ’yancin ’yan ƙasa, da kuma bin dokokin da suka dace.”
Hundeyin ya bayyana cewa direbobi da ke bukatar izinin gilashi mai duhu ana ƙarfafa su su neme ta ta hanyar da aka amince da ita kuma su tabbatar da cewa motocinsu sun dace da ka’idojin doka