Home NewsMDD ta nemi a saki mutum 10,000 da aka tsare ba bisa ƙa’ida ba a Eritrea

MDD ta nemi a saki mutum 10,000 da aka tsare ba bisa ƙa’ida ba a Eritrea

Majalisar Dinkin Duniya ta yi maraba da sakin ƴan Eritrean 13 da aka tsare kusan shekaru 18 ba tare da shari’a ba, inda ta bayyana hakan a matsayin ci gaba mai kyau, sannan ta yi kira ga hukumomin ƙasar da su saki duk sauran mutanen da aka tsare ba bisa ka’ida ba.

A wata sanarwa da aka fitar, MDD ta buƙaci Eritrea da ta saki duk wadanda suka rage a kurkuku ba tare da sharaɗi ba, ciki har da tsoffin manyan jami’an gwamnati da ak

MDD ta kiyasta cewa fiye da mutane 10,000 ne a ke tsare da su ba bisa ka’ida ba a Eritrea, ciki har da ‘yan siyasa da ‘yan jarida da shugabannin addini da dalibai.a kama a shekarar 2001 saboda kira na sauye-sauye a harkokin siyasa da shugabanci.

Gwamnatin Eritrea ta saki mutum 13 ɗin ne a ranar 4 ga Disamba, waɗanda suka haɗa da ‘yan kasuwa da jami’an ‘yan sanda da sauran ƙwararru da suke tsare a kurkukun soji na Mai Serwa kusan shekaru ashirin.

Haka kuma, majiyoyi daga cikin ƙasar da waje sun bayyana wa BBC cewa hukumomin sun kuma saki mabiya cocin da aka haramta guda 98, da dama daga cikinsu suna tsare tsawon shekaru.

You may also like

Leave a Comment