Home NewsGwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na kafa Sabon Sansanin Soji a Abakaliki da ke a jahar Ebonyi.

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na kafa Sabon Sansanin Soji a Abakaliki da ke a jahar Ebonyi.

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na kafa
Sabon Sansanin Soji a Abakaliki da ke a jahar
Ebonyi.

Matakin amincewar ya kara adadin defo din Soji
da ake da su a kasar nan zuwa guda uku baya ga
na Kaduna da na Osogbo da ake da su tunda
dadewa.

Mashawarcin shugaban Kasa Bola Tinubu a
dandalin sada zumunta Dada Olusegun ya
bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a
shafin sadarwa.

A wani fefen Bidiyo da aka fitar, Babban Hafsan
Rundunar Sojin Nigeria Major Janar Waidi
Shu’aibu ya bayyana cewa matakin na da
manufar karfafa Rundunar Sojin Nigeria adaidai
lokacin da ake fama da kalubalen tsaro a Kasar
nan.

Ya kara da cewa akwai karin Dakarun Sojin
Nigeria guda dubu Uku da Dari biyar da za a
horas da su a sabon Sansanin, baya ga wasu
guda dubu uku da dari Biyar suma da ake sa ran
isowarsu defo din soji da ke a Osogbo a makon
gobe.

A cewar Babban Hafsan Rundunar Sojin ta
Nigeria, Dakarun za su sami horon yaki tare da

amfani da fasahohin zamani da kuma kaifafa
tunaninsu.

You may also like

Leave a Comment