Home NewsWakilin shugaban Amurka Donald Trump a ƙasashen ƙetare zai tafi Jamus a ƙarshen wannan makon don ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da shugabannin ƙasashen Turai a zagayen ƙarshe na tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine da Rasha.

Wakilin shugaban Amurka Donald Trump a ƙasashen ƙetare zai tafi Jamus a ƙarshen wannan makon don ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da shugabannin ƙasashen Turai a zagayen ƙarshe na tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine da Rasha.

Wakilin shugaban Amurka Donald Trump a
ƙasashen ƙetare zai tafi Jamus a ƙarshen
wannan makon don ganawa da shugaban
Ukraine Volodymyr Zelensky da
shugabannin ƙasashen Turai a zagayen
ƙarshe na tattaunawa kan kawo ƙarshen
yaƙin Ukraine da Rasha.

Steve Witkoff, wanda ke jagorantar yunƙurin
White House na shiga tsakanin Ukraine da
Rasha, zai tattauna sabon daftarin
yarjejeniyar zaman lafiya da ake shirin yi a
Berlin.

Gwamnatin Trump dai na ƙoƙarin ganin an
cimma yarjejeniyar kafin lokacin Kirsimeti,
kuma ta gudanar da tattaunawa da dama da
wakilan Ukraine da na Rasha a cikin ƴan
makonnin da suka gabata, ko da yake ba a
ga alamar samun nasara ba.

Har yanzu dai ba a tabbatar da shugabannin
ƙasashen Turai da za su halarci tattaunawar
ta Berlin ba.

You may also like

Leave a Comment