215
Hukumomin Indiya sun ce ɗaya daga cikin yanbindigar da suka kashe mutum 15 a Bondi ranar Lahadi ‘dan Indiya ne.
Yansanda a kudancin jihar Telangana sun ce Sajid Akram ‘dan Hyderabad ne da ya koma Australia shekaru 27 da suka gabata.
Jami’ai a Australia na binciken abinda ya sa ƴan bindigar suka kwashe kusan wata ‘daya a Philipphines, inda aka jima da samun ɓillar masu iƙirarin jihadi.
Ana cigaba da matsawa hukumomin tsaro lamba anan inda suka yi bayanin alaƙar da ke tsakanin yan bindigar da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi.
Yan sandan Australia sun harbe ɗaya daga cikin ƴanbindigar yayin da rahotanni suka ce matashin ya farfado daga dogon suma a asibiti.