200
A ƙudurin da aka amince da shi yayin zaman, kwamitin ya yi Allah wadai da farmakin da ƙungiyar M23 ke kaiwa tare da zargin samun goyon bayan Rwanda, yana kuma buƙatar Kigali ta daina tallafa wa ƴan tawayen ta kuma janye dukkan dakarunta.
Ƙudurin ya kuma tabbatar da ci gaba da aikin rundunar MONUSCO da ke da sojoji kusan 11,500 a faɗin ƙasar.
Wannan ƙuduri ya zo ne yayin da M23 ta ce ta janye daga birnin Uvira bayan matsin lamba daga Amurka, sai dai gwamnatin Congo ta ce janyewar wasan kwaikwayo ce kuma ƴan tawayen har yanzu suna cikin birnin.