An saba duk shekara ana ganin sababbin fuskoki a fina-finan Kannywood, musamman tun bayan komawar harkar saka fina-finai masu dogon zango a YouTube.
A farko-farko an fi ganin matasa da ƙananan jarumai a fina-finai masu dogon zango, amma daga bisa manyan jaruman sun shiga ana damawa da su.
Haskar ta fuskanci ƙalubalen kasuwanci tun bayan da kasuwancin CD ya mutu murus, lamarin da ya karya masu shirya fina-finai da dama, kuma har yanzu wasu ba su gama farfaɗowa ba.
Kusan yanzu za a iya cewa masana’antar baki ɗaya ta koma fina-finai masu dogon zango kuma kasuwancin fina-finan ya koma YouTube, lamarin da ya taimaka wajen sake farfaɗo da masana’antar ta koma hayyacinta.
Sai dai duk da kasancewar manyan jarumai sun shiga fina-finan na YouTube ana damawa da su, ana ci gaba da samun sababbin fuskoki da suke samun tagomashi da ɗaukaka cikin ƙanƙanin lokaci.