Home NewsShugaban Taiwan Lai Ching-le ya lashi takobin kare ƙasar daga China

Shugaban Taiwan Lai Ching-le ya lashi takobin kare ƙasar daga China

Shugaban Taiwan Lai Ching-te, ya lashi takobin kare ‘yanci da martarbar yankinsa bayan China ta kaddamar da wani atisayen soji a kusa da yankin wanda China ke iƙrarin cewa nata ne.

Cikin saƙon sabuwar shekarar da ya gabatarwa ƴan ƙasar, Mr Lai ya yi alƙawarin ƙarfafa tsaron yankinsa.

Ya ce ƙasashen duniya na ganin ko al’ummar Taiwan za su iya kare kansu, inda ya nemi su yi aiki tare wajen ƙarfafa dakarunsu a daida lokacin da suke fuskantar barazana.

Mista Lai Ching-le ya kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi kasuwanci da haɗin kai tare da Amurka.

You may also like

Leave a Comment