Home NewsDokar Haraji: Shugaba Tinubu Na Yin Abin Da Gwamnatocin Baya Suka Kasa Yi — Sarkin Kano Sanusi II

Dokar Haraji: Shugaba Tinubu Na Yin Abin Da Gwamnatocin Baya Suka Kasa Yi — Sarkin Kano Sanusi II

Dokar Haraji: Shugaba Tinubu Na Yin Abin Da Gwamnatocin Baya Suka Kasa Yi — Sarkin Kano Sanusi II

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ɗaukar matakan da suka dace a batun haraji, matakan da gwamnatocin da suka gabata suka ƙi ko suka kasa ɗauka.

Sarkin ya ce gyaran tsarin haraji yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa, rage dogaro da bashi, da kuma tabbatar da adalci a tsakanin masu biyan haraji.

A cewarsa, duk da cewa sauye-sauyen na iya zama masu wahala a farko, amma su ne ginshiƙin gina ƙasa mai ɗorewa da tattalin arziki mai ƙarfi.

You may also like

Leave a Comment