Dalilan da suka sa aka ɗage komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf APC zuwa jam’iyyar APC.
Bayan shirye-shiryen farko sun kammala, an samu bayanai kan dalilan da suka sa aka ɗage shirin komawar Abba Kabir Yusuf jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A cewar rahotanni, an tsara Gwamna Abba ya zama na farko da za a yi wa rajista a Kano a sabon shirin rajistar APC ta yanar gizo, tare da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya raka shi zuwa Diso Ward domin karɓar katin membobinsa. Daga nan kuma a raka Ganduje zuwa Dawakin Tofa don sabunta rajistarsa.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Sai dai majiyoyi sun ce an dakatar da shirin ne bayan an ja hankalin gwamnan cewa ya dace ya fara ganawa da manyan jagororin APC a Kano—musamman Ganduje da Sanata Barau Jibrin—domin neman albarka kafin sanarwar sauya sheka.
“Idan gwamna ya koma APC ba tare da ganawa da Ganduje da Barau ba, hakan zai iya nuna raini ga shugabannin jam’iyyar, kuma ba zai masa anfani ba,” in ji wata majiya.
Duk da cewa an ambaci ranar 12 ga Janairu a matsayin ranar sanarwa, majiyoyi sun ce ranar na iya canzawa, kuma komawar za ta iya faruwa “duk lokacin da aka kammala ganawa da jagororin APC na Kano”.
Wasu majiyoyi sun kuma ce Bola Tinubu ne ya umarci a dakatar da lamarin domin a yi ƙoƙarin ƙarshe na jawo hankalin uban siyasar gwamnan, Sanata Rabiu Kwankwaso.
A cewarsu, yiwuwar Kwankwaso ya koma African Democratic Congress (ADC) ta sauya lissafin APC, musamman bayan jita-jitar haduwarsa da Olusegun Obasanjo da Peter Obi, abin da ke tayar da zargin haɗakar Obi/Kwankwaso a 2027.
“Ba tare da Kwankwaso ba, ƙarfin siyasar gwamnan na iya raguwa. A gaskiya, gwamnan ne ke neman APC, ba APC ke nemansa ba,” in ji wata majiya.
Sai dai wasu bayanai sun ce gwamnan da kansa ya nemi ƙarin lokaci domin ya shawo kan ’yan majalisar jiha da ta ƙasa su biyo shi.
A gefe guda kuma, rahotannin da ba a tabbatar ba sun nuna cewa tsananin martani daga magoya baya ya sa gwamnan ke tunanin dakatar da komawar gaba ɗaya, ya koma sasanci da jagoransa.