Home NewsGwamnatin Burkina Faso Ta Saki Sojojin Najeriya bayan Ganawa da Tuggar.

Gwamnatin Burkina Faso Ta Saki Sojojin Najeriya bayan Ganawa da Tuggar.

Gwamnatin Burkina Faso ta saki jami’an sojin saman Najeriya 11 bayan shafe kwanaki tara suna tsare, biyo bayan tattaunawar diflomasiyya mai zurfi da gwamnatin tarayyar Najeriya ta jagoranta. Sakin jami’an ya zo ne jim kadan bayan kammala ziyarar wata tawagar Najeriya a birnin Ouagadougou, wacce ta gudanar da tattaunawa da manyan jami’an Burkina Faso ciki har da shugaban kasa, Ibrahim Traoré.

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa matakin ya kawo karshen lamarin da ya ja hankalin masu lura da harkokin tsaro a yankin, tare da bude sabon babi na fahimta da jituwa tsakanin kasashen biyu.

Tawagar da ta wakilci Najeriya ta kunshi manyan jami’ai daga ma’aikatar harkokin waje, ma’aikatar tsaro da kuma hedikwatar rundunar sojin saman Najeriya. An ba tawagar wannan aiki ne domin neman mafita ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna, ba tare da dagula alaka ko kara tsamin dangantaka ba. Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa manufar ziyarar ita ce kwantar da hankula da kuma tabbatar da sakin jami’an da aka tsare ta hanyar lumana.

A cewar majiyar, wannan mataki ya nuna yadda Najeriya ke fifita diflomasiyya da kyakkyawar mu’amala da makwabta wajen warware matsaloli masu sarkakiya.

Majiyar ta ce ziyarar ta mayar da hankali kan nauyin da kasashen ke da shi na bai daya wajen tinkarar kalubalen tsaro a yankin Sahel. Haka kuma, tawagar ta jaddada kudirin Najeriya na bin ka’idojin kasa da kasa a harkokin sufurin jiragen sama da ayyukan soja.

Rahotanni sun nuna cewa Najeriya da Burkina Faso sun dade suna aiki tare a fannoni da dama na tsaro, ciki har da horaswa, musayar bayanan sirri da yunkurin wanzar da zaman lafiya a yankin Yammacin Afirka.

Kasashen biyu, tare da sauran mambobin kungiyar Sahel, sun sha haduwa wajen yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da ke barazana ga zaman lafiyar yankin.

Tribune ta rahoto cewa tawagar Najeriya ta yi amfani da damar wajen tuna wa hukumomin Burkina Faso irin wannan doguwar alakar hadin kai da ke tsakaninsu.

Jami’ai daga bangarorin biyu sun nuna kwarin gwiwa cewa warware wannan lamari cikin nasara zai kara zurfafa fahimta da amana a tsakanin kasashen.

Sun bayyana cewa wannan nasara za ta taimaka wajen karfafa hadin gwiwar tsaro da kokarin tabbatar da zaman lafiya mA wani labarin, kun ji cewa kafin sakin sojojin Najeriya da aka rike a Burkina Faso, dakarun sun nemi a kai musu dauki.

A korafin da suka yi, sun koka da cewa suna fargabar cewa za su iya yin bikin Kirsimeti a tsare a kasar Burkina Faso. Sai dai tun a lokacin, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce tana kokari wajen ganin sun dawo gida kafin Kirsimeti.

 

You may also like

Leave a Comment