931
Rahotonni daga Sudan na cewa hare-haren jirage marasa matuƙa sun faɗa jihar North Kordofan da ke tsakiyar ƙasar.
Kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasar ya ce ɗaya daga cikin hare-haren ya faɗa kan kamfanin a babban birnin jihar El-Obeid ranar Lahadi da safe, lamarin da ya haifar da katsewar lantarki a birnin, wanda sojoji ke iko da shi.
Hukumomi sun ce sun kakkaɓo wani jirgin maras matuƙi da maraicen ranar Asabar a jihar.
Yayin da rahotonni suka ce an kakkaɓo wasu da suka yi yunƙurin kai hari sansanin sojin sama da wani kamfani a kusa da jihar White Nile mai maƙwabtaka.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu da yawaitar amfani da jirage marasa matuƙa da duka ɓangarorin da ke yaƙi da juna a Sudan ke yi.