Mai shari’a Maryam Hassan ce ta bayar da wannan umarni yayin yanke hukunci kan buƙatar beli da aka shigar a madadin tsohon ministan, ta hannun lauyansa, Patrick Ikwueto, SAN.
A cikin hukuncin nata, Mai shari’a Maryam Hassan ta umarci Chris Ngige da ya gabatar da wanda zai tsaya masa, wanda dole ne ya kasance darakta a aikin gwamnatin tarayya tare da mallakar fili ko gida.
Kotun ta kuma umurci wanda zai tsaya masa da ya miƙa takardun mallakar filin ko gidan, da kuma takardun tafiyarsa na ƙasashen waje, a gaban kotu, har zuwa lokacin da Chris Ngige zai kammala dawo da
fasfot ɗinsa na ƙasashen waje.
Tun da farko, EFCC ta ba Ngige beli bisa amincewa da kansa, inda ta umarce shi da ya miƙa takardun tafiyarsa ga hukumar, tare da gabatar da wanda zai tsaya masa guda ɗaya.