281
Shugaban hukumar ta JAMB, Farfesa Is’haq Oloyede, ya bayyana hakan a Ilorin yayin zagayen tantance cibiyoyin.
Ya ce an tura masana 52 a jihohi daban-daban domin sake tantancewa cibiyoyin ko cire waɗanda ba su cika ƙa’idojin hukumar ba.
Ya ƙara da cewa aikin tantancewar yana tafiya yadda ya kamata, inda wasu cibiyoyi da aka taɓa samu da hannu a maguɗin jarabawa a baya suka sake bayyana, yayin da wasu suka sauya wurare domin ci gaba da aiki.