Home NewsMajalisar dattawa ta amince da naɗin mutum uku na farko da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata domin tantancewa a matsayin jakadun Najeriya a ƙasashen waje.

Majalisar dattawa ta amince da naɗin mutum uku na farko da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata domin tantancewa a matsayin jakadun Najeriya a ƙasashen waje.

Sabbin jakadun da majalisar ta amince da naɗin nasu su ne Aminu Muhammad Dalhatu daga Jihar Jigawa, Lateef Kayode Kolawole Are daga Jihar Ogun, da kuma Emmanuel Ayodele Oke, CFR, daga Jihar Oyo.

Majalisar ta amince da naɗin ne bayan la’akari da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan harkokin waje, wanda ya gudanar da tantancewar waɗanda aka gabatar a makon da ya gabata.

Sai dai har yanzu akwai ragowar wasu 64 da shugaba Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa, waɗanda aka tantance amma ba a kai ga tabbatar da naɗin nasu ba.

You may also like

Leave a Comment