Home NewsRundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta yi nasarar warware wani bam da aka dasa ƙarƙashin turken kamfanin sadarwa a unguwar Federal Low Cost, dake Maiduguri.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta yi nasarar warware wani bam da aka dasa ƙarƙashin turken kamfanin sadarwa a unguwar Federal Low Cost, dake Maiduguri.

Rahotanni sun bayyana cewa an gano bam ɗin ne bayan da wasu mazauna yankin suka lura da wani abin da ke da shakku, suka kuma sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Bayan samun rahoton, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Borno, Naziru Abdulmajid, ya bayar da umarnin tura Tawagar kwararru domin ɗaukar matakin gaggawa.

Jami’an tsaron sun killace yankin gaba ɗaya, tare da bin ƙa’idojin tsaro, sannan suka warware bam ɗin cikin nasara.

Binciken farko ya nuna cewa bam ɗin na da girman haɗarin da zai iya haifar da rasa rayuka idan da ya fashe.

A wajen da aka warware bam ɗin, an kuma gano almakashi da riga da takalmi, lamarin da ke nuna yiwuwar waɗanda suka aikata laifin sun tsere daga wurin kafin zuwan jami’an tsaro.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa ta ƙara tsaurara sintiri da tsaro a muhimman wurare  tare da jan hankalin jama’a da su kasance masu lura, sannan su kuma gaggauta kai rahoto idan sun ga wani abu da ke da alamar barazana.

A halin yanzu,ana cigaba da gudanar da harkokin yau da kullum a yankin.

You may also like

Leave a Comment