424
Rundunar sojin kudancin Amurka ta wallafa faifan bidiyon hare-haren a shafukan sada zumunta, inda ta ce jiragen na tafiya ne ta hanyoyin da aka san ana safarar miyagun ƙwayoyi, kuma suna cikin ayyukan safarar kwayoyi.
A cewar sojojin, sama da jiragen ruwa 20 a Tekun Pasifik da na Caribbean aka kai wa hare-hare a ‘yan watannin nan, inda aƙalla mutum 90 suka rasa rayukansu.
Wannan wani ɓangare ne na tsaurara matakan da shugaba Donald Trump ke ɗauka kan ƙungiyoyin da ya ke zargi da safarar kwayoyi zuwa yankin.
Sai dai wasu masana sun ce waɗannan hare-hare na iya saɓawa dokokin yaƙi na kasa da kasa.