Ministan aiyuka David Umahi ya musanta kiraye-kirayen kafa Kasar Biafara a bisa ga yadda shugaban Kasa Bola Tinubu ya shigar da al’ummar Igbo a cikin tsarin cigaban Kasa.
Umahi ya bayyana hakanne ayayin dubu aiyukan da gwamnatin tarayya ta ke gudanarwa a shiyyar Kudu maso gabashin Njgeria.
A cewarsa kiraye-kirayen son zuciya na cewa an mayar da shiyyar Kudu maso gabas saniyar ware a fannin cigaba, shi ya haifar da bullar ‘Yan Aware, sai dai ya ce a halin yanzu hakan ya ragu a saboda samuwar aiyukan gwamnatin tarayya a bangaren gina tituna da samar da ababan more rayuwa a fadin shiyyar Kudu maso gabashin Nigeria.
Ministan ya bayyana jerin sunayen aiyukan gwamnatin tarayya da ake yi da kuma wadanda aka kammala a shiyyar kudu maso gabas wadanda duk a baya aka tsayar da aiyukansu har sai bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi ragamar tafiyar da kasar nan sannan aka cigaba da su a halin yanzu.