Home NewsGwamnan Jahar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da a kashe naira Biliyan Uku da Miliyan dari bakwai da Saba’in a bangaren ilimi da ya hadar da gyaran makarantu da samar da kayan koyo da koyarwa da kuma biyan ‘Yan kwangila da masu samar da kayan aiki, kudadensu a fadin jaharnan.

Gwamnan Jahar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da a kashe naira Biliyan Uku da Miliyan dari bakwai da Saba’in a bangaren ilimi da ya hadar da gyaran makarantu da samar da kayan koyo da koyarwa da kuma biyan ‘Yan kwangila da masu samar da kayan aiki, kudadensu a fadin jaharnan.

Matakin amincewar an cimma shi ne ayayin taron majalisar zartaswa na jahar Kano karo na 35 da ya gudana a ranar 18 ga watan Disamban shekarar 2025.

A cewar gwamna Abba kabir Yusuf an amince da a kashe naira biliyan daya da miliyan dari shida da Casa’in wajen biyan ‘Yan kwangilar da ke samar da abinci a makarantun kwana a zangon karatu na shekarar 2025 zuwa 2026, a inda kuma aka ware naira miliyan dari uku da Saba’in da Biyar wajen sayo kayan karatun Dalibai da su ka hadar da Jakankunan Makaranta ga Dalibai a fadin jahar Kano.

Hakanan Majalisar ta amince da akashe naira miliyan dari uku da sittin da tara da dubu dari tara wajen gyaran makarantar sakandaren Mariri da kuma kudi naira biliyan daya da miliyan dari uku da Ashirin wajen Sauya matsuguni ga makarantar Sakandaren Mai Kwatashi da kuma Makarantar Firamaren Dan-Waire wadanda aiyukan kyautata muhalli duk ya shafe su.

You may also like

Leave a Comment