Home PoliticalRahotannin da ke cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC an dage shi zuwa wata ranar saɓanin ranar Litinin da aka bayyana tun da farko.

Rahotannin da ke cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC an dage shi zuwa wata ranar saɓanin ranar Litinin da aka bayyana tun da farko.

Rahotannin da ke cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC an dage shi zuwa wata ranar saɓanin ranar Litinin da aka bayyana tun da farko.

Jaridar PlatinumPost ta rawaito cewa majiyoyi kusa da gwamnan sun bayyana cewa ranar da aka fara tsara wa domin sauyin sheƙar a hukumance, wato Litinin, 5 ga Janairu, 2026, yanzu an sauya ta zuwa Litinin, 12 ga watan Janairu, 2026.

A baya, dai jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa daga NNPP zuwa jam’iyyar APC a ranar 5 ga Janairu, 2026.

Sai dai wata majiya mai tushe, wadda ta nemi a sakaya sunanta kuma ta halarci wani taro tsakanin Gwamna Yusuf da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a Abuja ranar Juma’a, ta bayyana cewa gwamnan ya nemi ƙarin lokacin sauya sheƙar.

A cewar majiyar, Yusuf na son ci gaba da tuntubar wasu ‘yan majalisar dokokin jihar da sauran manyan masu ruwa da tsaki da har yanzu ba su bayyana cikakken goyon bayansu ga wannan yunƙurin siyasa ba na sauya sheƙar zuwa APC.

You may also like

Leave a Comment