Home NewsBabban Hafsan Rundunar Sojin Nigeria Laftanal Kanal Waidi Shu’aibu ya jaddada Kudirin Rundunar Sojin Nigeria na ba da fifiko ga walwala da kuma kare Kimar hasoshin soji da kuma Dakarun sojin Kasar nan.

Babban Hafsan Rundunar Sojin Nigeria Laftanal Kanal Waidi Shu’aibu ya jaddada Kudirin Rundunar Sojin Nigeria na ba da fifiko ga walwala da kuma kare Kimar hasoshin soji da kuma Dakarun sojin Kasar nan.

Shu’aibu ya bayyana hakanne a birnin Ibadan na jahar Oyo ayayin Kaddamar da sabbin gidaje guda 60 da Dakarun Soji za su iya mallaka akan farashi mai rahusa da kuma rukunin wasu gudajen da shagunan kasuwanci wadanda bayan Soja ya kammala aiki zai iya mallakar su a yankin Akobo.

A cewarsa shirin samar da gidajen ya nuna aniyar Rundunar Sojin Nigeria na kulawa da walwalar Sojojin Kasar nan inda ya ce Rundunar za ta cigaba da zuba jari a bangaren kulawa da walwalar Dakarun soji domin kara karfafa musu guiwa ayayin aiki da kuma bayan sun kammala aikinsu.

Babban hafsan Rundunar Sojin na Nigeria ya ce shirin samar da gidajen an tsara shi ne domin tabbatar da cewa kowanne Jami’in Soja ya kammala aiki cikin kima da daraja tare da tallafa masa ya mallaki muhalli a duk wurin da ya zaba a fadin kasar nan.

You may also like

Leave a Comment