Home NewsYadda mata ke sauya akalar tsaro a Kano

Yadda mata ke sauya akalar tsaro a Kano

Wannan ya taka rawa wajen taƙaita damarsu ta shiga irin waɗannan ayyuka. Idan ma suka shiga, galibi suna taƙaita ne ga aikin zaman ofis ne ko na bayan fage.

Aikin ɗamara ko na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma an fi danganta su da maza saboda tasirin al’ada da addini. Wannan ne ya sa yawanci, idan mace ta shiga aikin tsaro, ake mata wani kallo na daban

 

Sai dai da alama gwamnatin Kano ta hango giɓin da hakan ya haifar ga tsaron jihar, da kuma irin gudummawar da mata za su iya bayarwa wajen shawo kan matsalolin satar mutane, ƙwacen waya da satar ababen hawa.

Gwamnatin ta ɗauki mata 130 daga cikin jami’ai 2,000 da ta bai wa horon tabbatar da tsaron rayuka da kuma samar da bayanan sirri a matakin unguwanni, wato NWC, a cikin matakanta na ƙarfafa tsaro daga tushe, ta hanyar amfani da mutanen da suka san unguwanni, hanyoyi da al’adun jama’a sosai.

Binciken Aminiya ya gano cewa shirin horas da jami’an NWC ya fara ne tun a watan Mayun shekarar da ta gabata, inda aka tantance mutane da dama, aka gudanar da gwajegwajen lafiyar jiki da tunani, tare da horaswa mai tsanani ƙarƙashin kulawar jami’an tsaro na gwamnati, ciki har da sojoji da ’yan sanda.

You may also like

Leave a Comment