Home NewsSojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan ‘Yan Ta’adda a Borno

Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan ‘Yan Ta’adda a Borno

Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan ‘Yan Ta’adda a Borno,

 

10 Jan 2026 ‘

 

Yan ta’adda sun ji babu dadi bayan dakarun sojojin sama sun yi musu ruwan wuta a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas Dakarun sojojin saman sun jefa bama-bamai kan maboyar ‘yan ta’addan da ke yankin Abbaga Jiri a Timbuktu Triangle Bama-baman da sojojin suka jefa kan ‘yan ta’addan sun yi nasarar kashe tsageru da dama tare da lalata wuraren boye kayan aikinsu

 

Sojojin Sama na Najeriya da ke aiki a karkashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai, sun kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a Borno. Sojojin sun samu nasara bayan kai harin sama na musamman kan ‘yan ta’adda a yankin Abbaga Jiri, cikin yankin Timbuktu Triangle na jihar Borno. Jiragen sojojin saman Najeriya a sararin samaniya Hoto: Sodiq Adelakun Source: Getty Images Jaridar Vanguard ta ce daraktan hulɗa da yaɗa labarai na hedikwatar sojojin sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar 10 ga watan Janairun shekarar 2026. KARA KARANTA WANNAN Nentawe: Shugaban APC ya kausasa harshe kan hare haren ‘yan ta’adda a Neja Sojojin sama sun samu nasara kan ‘yan ta’adda Ya ce nasarar ta samu ne bayan bayanan sirri daga tushe da dama da suka tabbatar da kasancewar ’yan ta’adda, gine-ginensu, da kuma wuraren ɓoye kayan aiki a yankin. A cewar sanarwar, bayan tabbatar da sahihin bayanan sirri, jiragen sojojin sama sun shiga aiki ta hanyar leken asiri da kuma kai hare-haren da suka dace kan wuraren da aka gano. “An kai farmaki ne domin raunana karfin ’yan ta’adda, hana su samun mafaka, da kuma share wa sojojin kasa hanya, tare da bin ka’idojin aikin soja da kuma kare rayukan fararen hula.

 

Ehimen Ejodame Babban hafsan sojojin sama ya yi tsokaci Da yake tsokaci kan nasarar aikin, Babban hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sunday Aneke, ya ce nasarar ta nuna kudirinsu na mamaye sararin samaniya domin tallafa wa ayyukan haɗin gwiwa na sojoji, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da hakan. “Wannan aiki ya nuna jajircewarmu ta amfani da kayan aiki cikin tsari da daidaito domin tallafa wa sojojin kasa. Za mu ci gaba da hana ’yan ta’adda samun ’yancin motsawa, wuraren ɓoyewa da hanyoyin samun kayan aiki a duk inda suka buya.

You may also like

Leave a Comment