100
Da ƊUMI-ƊUMI: Babu Wata Barazana Da Za Ta Girgiza Iran, Lamura Na Karkashin Iko – Ministan Harkokin Waje
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa halin tsaro da siyasa a ƙasar na karkashin cikakken iko, duk da rikice-rikicen da ake fuskanta a kwanakin nan.
A cewarsa, katsewar intanet da aka yi na ɗan lokaci ne kawai domin dalilan tsaro, kuma gwamnati na aiki tukuru don mayar da intanet ga al’umma nan ba da jimawa ba.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa da duniya cewa babu wata barazana da za ta girgiza Iran, yana mai cewa hukumomi sun shirya tsaf domin kare rayuka da dukiyar jama’a.