177
Kwankwaso ya yi kira ga mabiya su kwantar da hankalinsu
Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya da su kasance masu haɗin kai da natsuwa a wannan lokaci. Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a bayan ya gudanar da wata ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki na tafiyar tasa.