Sabon harin Rasha da makamin Oreshnik ya kashe gwamman mutane a Ukraine
Sabbin hare-haren Rasha a Ukraine tun daga daren jiya Alhamis zuwa yau juma’a, ta hanyar amfani da makami mai linzami na Oreshnik, ya hallaka tarin mutane a Kyiv.
09/01/2026 – 16:20
Harin Rasha a Ukraine ya jefa mutane da dama cikin dubu
Harin Rasha a Ukraine ya jefa mutane da dama cikin dubu © Yan Dobronosov
Ma’aikatar tsaron Rasha ce ta sanar da ƙaddamar da sabbin hare-haren cikin wata sanarwa da ta fitar.
Dama shugaba Volodymr Zelensky ya yi gargaɗi a daren Alhamis cewa, akwai yiwuwar Rashan ta ƙaddamar da munanan hare-hare a ƙasar, bayan Moscow ta ƙi amincewa da wani tsari da shugabannin Turai su kai na girke dakarun haɗin gwiwa a Ukraine bayan ƙarewar yaƙin.
Dakarun Rasha sun ƙaddamar da harin makamai masu linzami 36 da jirage marasa matuƙa 242 a Ukraine cikin dare, kamar yadda rundunar tsaron saman Kyiv ta sanar yau Juma’a.
Ukraine ta ce ta samu nasarar kakkaɓo jirage marasa matuƙa 226 da makamai masu linzami 18 da Moscow ta harbo.
Harin na Rasha ya lalata gine-gine guda 20, da ofishin jakadancin Qatar a Kyiv, a cewar wani saƙo da Zelensky ya wallafa a shafinsa na X.
Tuni aka umarci mazauna yankin su fice da Kyiv bayan harin na Rasha, a wani yanayi da ake fuskantar tsananin sanyi.
A martaninta, ita ma Ukraine ta ƙara tsananta kai hare-hare kan gine-ginen makashi na Rasha, lamarin da ya jefa mutane dubu 556,000 cikin duhu a yankin Belgorod, wanda ke da iyaka da birnin Kharkiv na Ukraine.