Hukumar kula da ingancin Abinci da magunguna ta Ƙasa, NAFDAC, ta lalata wasu magunguna da na’urori na bogi waɗanda kimarsu ta kai sama da Naira miliyan dubu 55.
An gudanar da aikin lalata kayan ne a Ƙaramar Hukumar Akinyele da ke Jihar Oyo, a wani mataki na kare lafiyar al’umma daga haɗarin amfani da magunguna da kayan lafiya marasa inganci.
Kayayyakin da aka lalata sun haɗa da magunguna na bogi da waɗanda wa’adinsu ya ƙare da Na’urorin asibiti marasa inganci da Kayan kwalliya da abinci da ba su cika ƙa’idojin NAFDAC ba
Hukumar ta NAFDAC ta bayyana cewa an kama yawancin kayan ne daga masu shigo da su, da masu rarrabawa wasu kuma a kamfanonin da ake samar da su yayin da wasu kuma kamfanoni da ƙungiyoyi sama da 70 suka miƙa su da kansu bayan an gano ba su dace da amfani ba.
Daraktar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce matakin ya zama dole domin kare rayukan al’umma, inda ta jaddada cewa hukumar ba za ta yi sassauci ga duk wanda aka samu da laifin ƙera ko sayar da magungunan bogi ba.
Ta kuma yabawa haɗin gwiwar hukumomin tsaro da suka haɗa da ‘Yan Sanda, Kwastam, DSS, NDLEA, NSCDC da sauran su, wajen tabbatar da nasarar aikin.
NAFDAC ta yi kira ga jama’a da su guji sayen magunguna daga wuraren da ba a amince da su ba, tare da sanar da hukuma duk wani zargi da suke da shi domin a dauki matakin da ya dace.