Home NewsKotu ta aike da Sheikh Makwarari, gidan gyaran hali kan zargin harƙallar filaye

Kotu ta aike da Sheikh Makwarari, gidan gyaran hali kan zargin harƙallar filaye

A ranar Laraba 21 ga Janairu, 2026, ne dai kotun ta fara sauraron wata shari’a wadda ƴansanda su ka gurfanar da Malamin bisa zargin da harƙallar filaye.

A yayin zaman kotun na yau, an tafka muhawara tsakanin mai gabatar da ƙara da lauyan wanda ake zargin.

Lauyan wanda ake tuhuma ya bayyana cewar, akwai wata shari’a irin wannan a gaban babbar kotun jahar Kano.

A karshe dai an karanta kunshin zargin inda tuhumar ta bayyana cewar, Ibrahim Abdullahi Isa makwarari, a na zargin sa da laifin buga takaddar fili ta jabu.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, takardun shaidar mallaka da Ibrahim Makwarari ya gabatar mai ƙunshe da sunan Kasim Ibrahim Baba, da Ibrahim Abdullahi Isah, takardu ne da ba su da inganci.

A yayin zaman dai, an samu taƙaddama akan wani fili da ke Ahmadu Bello Way, wanda ya ke a matsayin mallakin Abdu Yaro Fagge, kamar yadda ma’aikatar ƙasa ta bayyana, don haka binciken yansanda ya gano cewar waccan takadda ta hannun Makwarari ba ta da alaƙa da wannan fili na Ahmadu Bello way.

A cikin takardar, ma’aikatar ƙasa ta bayyana cewar waɗannan takardu ba su da inganci, kuma ba su da wata alaƙa da wancan fili da ake magana a kan sa.

Yayin da aka karanta kunshin zargin Ibrahim Makwarari ya musanta.

Lauyan da yake kare shi ya roki kotun da cewar ta bayar da belin wanda ake tuhuma kasancewar laifin da ake zargi ya faɗo cikin hurumin wannan kotun, za kuma su cika duk wani sharadi da kotun za ta sanya.

Sai dai mai gabatar da kara ya yi suka inda ya bayyana cewar yansandan sun rubuta takaddar tuhuma tun watan 12 na shekarar da ta gabata ta 2025, kuma wanda ake tuhuma ya san cewar akwai takaddun tuhuma a gaban wannan kotun amma ya na ta kawo tarnaki a kan shari’ar domin haka yake kyautata zaton cewar idan aka bayar da belin zai iya yin katsaladan akan yadda za a saurari shari’ar.

Mai gabatar da ƙara ya ƙara bayyana cewar, sun yi ta buga masa waya tsahon watanni uku domin ya zo a je kotu amma abin ya faskara.

Mai gabatar da kara ya kara da cewar yayin da wanda ake tuhuma ya ki zuwa domin a gurfanar da shi, yansanda sun roki kotu da ta ba su umarnin kamo shi, kuma yansanda sun kama shi a jiya harma a yayin kamun ya bayyana cewar babu wanda ya isa ya kai shi kotu, don haka suke yin suka a kan batun bayar da belin.

Lauyan wanda ake tuhuma ya bayyana cewar, mai gabatar da ƙara bai kawo hujja akan doka ba a don haka ya roƙi a yi watsi da sukar da ya yi.

Kotun ta bayar da beli mutum biyu, ɗayan dole ya zama mai sarautar gargajiya tare da samun takaddar shaidar naɗin sa daga fadar sarkin Kano, sai kuma wani mutum ɗaya fitacce mai gida a Kano, idan kuma wanda ake tuhuma ya tsere masu karɓar belin za su biya Naira miliyan 20, kotun ta sanya ranar 12 ga watan Fabrairu, 2026.

Tuni dai kotun ta aike da Sheikh Ibrahim Isah Makwarari, gidan gyaran hali sakamakon gaza cika sharuɗan beli kan zargin da ake yi masa.

You may also like

Leave a Comment