Shugaban ƙasar ya bayar da umarnin ne a ranar 24 ga watan
Nuwamba, a wani ɓangare na ƙoƙarin fuskantar matsalolin tsaro da ke
ƙaruwa a faɗin ƙasar, musamman sace-sacen mutane a wasu jihohin
Arewa.
Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa an umarci
jami’an Hukumar Sibil Difens, NSCDC, su karɓi ayyukan tsaron manyan
jami’ai daga hannun ’yan sanda.
Cikin aiwatar da umarnin, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode
Egbetokun, ya ce an janye jami’an ’yan sanda sama da dubu goma sha ɗaya daga aikin tsaron VIP, tare da sake tura su ayyukan tsaron al’umma.
Sai dai bayan wannan mataki, wasu fitattun ’yan Najeriya sun fara
neman jami’an NSCDC da kamfanonin tsaro masu zaman kansu domin
tsaron kansu.
Haka kuma, bincike ya nuna cewa wasu jami’an DSS sun fara tuntuɓar
manyan jami’ai, suna neman a roƙi daraktocin DSS na jihohi da a tura
su a matsayin sabbin masu tsaron kansu.
Wani babban jami’in DSS ya bayyana cewa yawancin jami’an da ke
neman irin wannan aiki ƙananan ma’aikata ne, yana mai cewa hukumar
na da tsauraran ƙa’idoji kan tura jami’anta wajen manyan jami’ai.
Ya ƙara da cewa sabon Darakta Janar na DSS, Adeola Ajayi, ya kawo
ƙarshen duk wani tura jami’ai ba bisa ƙa’ida ba, inda ya nuna cewa
jami’an da suka haura mataki na goma sha uku ba a tura su aikin tsaron
VIP sai ga gwamnoni ko fadar gwamnati a Abuja.
Wani jami’in DSS kuma ya jaddada cewa tsaron manyan jami’ai na
daga cikin ayyukan da doka ta ɗora wa hukumar, sai dai ya gargaɗi
jami’ai da kada su nuna matsanancin kwaɗayi wajen neman irin
waɗannan mukamai.
Bayan umarnin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar na janye ’yan sandan da ke aikin tsaron manyan jami’ai da ’yan siyasa, rahotanni sun nuna cewa wasu jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, sun fara kamun kafa domin maye gurbin yan sandan dake baiwa manyan mutane tsaro.
400