669
Yadda ‘yan bindiga suka hana al’ummar Ƙaramar Hukumar Borgu a jihar Neja sakat
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da cewa wasu ‘ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Damala da ke garin Woko a Karamar Hukumar Borgu ta jihar, inda suka kashe aƙalla mutum hudu.
Harin, wanda aka kai a makon da ya wuce, ya zo ne mako guda bayan da wasu ‘yan bindigar suka kashe mutane 42, ciki har da na kasuwar Daji da ke ƙauyen Demo, a ƙananan hukumomin Borgu da Agwara da ke makwabtaka da juna.
Mazauna yankunan karamar hukumar sun shaida wa BBC cewa suna zaune cikin fargaba da tashin hankali a kullum.
Mazauna yankunan sun ce saboda hare-haren da ‘yan binidgan ke kai wa a yanzu akwai wasu kasuwanni yankin da aka rufe.