Home NewsGwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya yaba wa rundunar sojin ƙasar bisa kafa cibiyar horar da sojoji a jihar.

Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya yaba wa rundunar sojin ƙasar bisa kafa cibiyar horar da sojoji a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, a fadar gwamnatin jihar da ke Osogbo, gabanin bikin fitar da sabbin Sojoji rukuni na farko da aka horas a wannan cibiya.

Ziyarar ta babban hafsan sojin ƙasa, ta zo ne a matsayin wani bangare na shirye-shiryen bikin fitar da sabbin sojojin, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 20 ga Disamba, 2025.

Bikin na daga cikin manyan nasarorin faɗaɗa tsarin horaswa da bunƙasa ƙarfin sojojin ƙasa na Najeriya. A cikin wata sanarwa da mukaddashiyar Daraktar hulɗa da jama’a ta rundunar Sojin ƙasa, Kanal Appolonia Anele, ta fitar, ta ce bikin fitar da sojojin ya biyo bayan umarnin Shugaban Ƙasa na ayyana dokar ta-baci kan tsaro, inda aka umarci rundunonin tsaro su ƙara ɗaukar ma’aikata da horas da su tare da tura sojoji masu cikakken shiri domin fuskantar barazanar tsaro a faɗin ƙasar nan.

A yayin ziyarar, janar waidi shu’aibu ya yaba wa gwamnatin jihar Osun bisa cikakken goyon baya da haɗin kai da suka bayar, wanda ya taimaka wajen kafa cibiyar cikin nasara.

Ya bayyana cibiyar a matsayin babbar kadarar ƙasa, wadda za ta ƙarfafa ayyukan sojoji tare da bayar da gudunmawa ga bunƙasa matasa da tabbatar da zaman lafiya.

Laftanar Janar Shaibu ya jaddada aniyar rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da bin ƙa’idojin bisa ƙwarewa da ladabi da biyayya, daidai da ingantaccen horaswa da suka samu, inda ya ce sabbin sojojin da ke kammala horaswa sun shirya tsaf domin shiga ayyukan tsaro a sassan ƙasar nan.

You may also like

Leave a Comment