Home BusinessGwamnatin Najeriya ta bayyana shirin ɗaukar sama da jami’an tsaro 90,000 a wani sabon mataki na ƙarfafa yaki da matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar ƙasar.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin ɗaukar sama da jami’an tsaro 90,000 a wani sabon mataki na ƙarfafa yaki da matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar ƙasar.

A ƙarƙashin wannan tsarin, hukumar ƴansandan Najeriya (NPF) za ta ɗauki ’yan sanda 50,000 ƙarin da za a haɗa da adadin da ake da shi yanzu.

Za a buɗe kafar ɗaukar aikin daga ranar 15 ga wannan wata na Disamban zuwa 25 ga watan Janairun 2026.

Wannan mataki ya biyo bayan wani shiri da gwamnatin ta soma tun farko na ɗaukar jami’an tsaro 30,000, waɗanda suka haɗa da ma’aikatan gidajen gyaran hali, ma’aikatan kula da iyakoki (Immigration), da wasu sassan tsaro daban-daban.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara a sassan Najeriya

You may also like

Leave a Comment