Home NewsZa mu maraɓci Obi idan ya koma LP bayan rasa tikitin shugaban ƙasa a ADC – Datti

Za mu maraɓci Obi idan ya koma LP bayan rasa tikitin shugaban ƙasa a ADC – Datti

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, ya ce za su sake tarbar Peter Obi idan ya koma jam’iyyar bayan rasa tikitin taƙarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC.

Datti ya bayyyana haka ne ranar Juma’a yayin tattaunawa a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels, inda ya ce zai fi kyau Obi ya koma jam’iyyar da ya yi wa taƙarar shugaban ƙasa a 2023.

“Na faɗa cewa idan Obi bai samu tikiti a ADC ba, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake maraɓtarsa idan ya dawo Labour Party,” in ji Datti.

“Zan tsaya tsayin daka wajen ganin babu wanda zai yi wa Obi abu mara kyau.

Kalamansa na zuwa ne bayan Obi ya sanar da komawa haɗakar African Democratic Congress, shekara uku bayan sun yi taƙarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar Labour.

Datti ya ce yana alfahari kan abin da suka cimma tare da Obi.

Ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa yana shirin fita daga Labour Party, inda ya ce labarin kanzon ƙurege ne.

You may also like

Leave a Comment