Home NewsAn kashe manoma 7 a sabon harin ‘yan bindiga a Filato

An kashe manoma 7 a sabon harin ‘yan bindiga a Filato

A cewarsa, harin ya zo ne duk da cewa tun da farko an samu gargadin tsaro da ya nuna cewa wasu al’ummomi a Jos ta Kudu suna cikin barazana.

“Bisa ga majiyoyin yankin, wannan mummunan lamari ya faru duk da gargadin tsaro da aka bayar tun da farko cewa wasu al’ummomi a karamar hukumar Jos ta Kudu LGA na iya fuskantar hare-hare,” in ji Tengwong.

“Abin bakin ciki, yanzu garin Bum ya fada cikin wannan sabon tashin hankali. Wannan hari ya ƙara a kan jerin hare-haren da ake kai wa al’ummomin karkara marasa da ba su ji ba, ba su gani ba a Jihar Filato, lamarin da ya ƙara tayar da hankali kan tsaron rayuka da dukiyoyi, musamman a lokacin bukukuwa da ya kamata a yi zaman lafiya da shagali.”

Ya ƙara da cewa ƙungiyar na bin diddigin abin da ke faruwa a yankin, kuma za ta ci gaba da sanar da jama’a yayin da karin bayanai ke dada fitowa.

“Ƙungiyar matasan Berom na bin diddigin lamarin sosai, kuma za ta ci gaba da sanar da jama’a yadda abubuwa ke gudana,” in ji shi.

Koƙarin samun martani daga hukumomin tsaro gaza har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto.

Kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Manjo Samson Zhakom, da na rundunar ’yan sandan Jihar, SP Alabo Alfred, ba su amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi ba dangane da lamarin.

You may also like

Leave a Comment