Furucin kungiyoyin na zuwa ne yayin gudanar da zanga zangar lumana da kungiyar ta gudanar a jihohin Zamfara, Bauchi, da Cross River, da Filato da sauran su.
Da yake jawabi yayin jagorantar zanga zangar a jihar Cross River, Shugaban kungiyar ta NLC na jihar Comrade Greg Olayi bayyana takaici yayi game da tabarbarewar tsaro da kasar nan ke fama da shi.
Yace mafi yawan ma’aikatan kasar nan ba sa samun sukunin gudanar da ayyukan su cikin nutsuwa, inda ya bada misali da haren haren da ake kaiwa makarantu da manoma da barazanar da matafiya ke fuskanta a hanyoyi.
A jihar Zamfara kuwa, shugaban kungiyar ta NLC Comrade Sani Halilu, bayyana irin halin matsalar tsaron da jihar ke fama da shi yayi, inda yace matakin ya Kai ga gurgunta fannoni daban daban na rayuwa.
Da yake jagorantar masu zanga zangar zuwa fadar gwamnatin jihar da ke Gusau tare da Mika takardar sakon su ga Gwamna Dauda Lawal, Comrade Halilu yace sun shirya zanga zangar ne domin nuna damuwa game da halin da kasar ke ciki na matsalar tsaro.
Da yake Mai da jawabi, gwamnan jihar ta Zamfara Dauda Lawal, yabawa shugabancin kungiyar kwadagin yayi bisa yadda suka nuna halin dattako da nutsuwa yayin gudanar da zanga zangar.