Home NewsMajalisar Dokoki ta kasa ta kafa kwamiti mai mutane 7 da zai duba zargin bullar Banbance- banbance a tsakanin rahoton da gwamnatin tarayya ta fitar akan Dokokin tattara haraji na kasa da kuma bayanan dokokin tattara haraji na kasa da majalisa ta amince da su tun da farko.

Majalisar Dokoki ta kasa ta kafa kwamiti mai mutane 7 da zai duba zargin bullar Banbance- banbance a tsakanin rahoton da gwamnatin tarayya ta fitar akan Dokokin tattara haraji na kasa da kuma bayanan dokokin tattara haraji na kasa da majalisa ta amince da su tun da farko.

Shugaban Majalisar wakilai ta tarayya Tajuddeen Abbas ya bayyana hakan bayan fuskantar tayar da Jijiyoyin wuya a zauren majalisa akan zarge- zargen cewa akwai Bambance-bambance a tsakanin Bayanan dokokin tattara haraji da gwamnatin tarayya ta fitar da kuma Bayanan dokokin tattara haraji da majalisa ta yi muhawara akai tare da amincewa da su.

Dan majalisar wakilai ta tarayya Abdussamad Dasuki daga Jahar Sokoto shi ya fara bankado zarge-zargen inda ya ce akwai sauye-sauye a Sadarorin dokokin tattara harajin wadanda kokadan ba a ma yi muhawara kokuma amincewa da su ba a zauren majalisa wanda daga ciki akwai tanade-tanaden yadda za a samar da wasu kudaden tafiyarwa.

A cewar Dan majalisar hakan ya ci karo da tanadin kundin tsarin mulki tare da keta hurumin majalisa, a donhaka ya ce daftarin dokokin na tattara haraji ba su yi daidai da wadanda Majalisar Dattawa da ta wakilai su ka yi muhawara tare da amincewa da su ba.

Akan haka ne shugaban Majalisar wakilai ta tarayya Tajudden Abbas ya amince da kafa kwamiti mai mutane bakwai a bisa Jagorancin Mukhtar Betara domin hada hancin dokokin na tattara haraji na kasa da bayanan rahoton majalisa akan dokokin, da kuma kwafin bayanan da gwamnatin tarayya ta fitar domin tantance girman sauye-sauyen da ake zargi akai.

Ya na daga cikin nauyin da aka dorawa kwamitin cewa ya gano ko an keta tanade- tanaden Kundin tsarin Mulki da kuma Ikon majalisa wanda daga nanne majalisa ta ce za ta san matakin da za ta dauka na gaba kafin fara aiwatar da dokokin na tattara haraji a cikin watan Disamba na sabuwar shekarar 2026.

You may also like

Leave a Comment