Home NewsTaƙaddama ta ɓarke tsakanin hukuma da Ƙungiyar CAN da al’ummar Kajuru

Taƙaddama ta ɓarke tsakanin hukuma da Ƙungiyar CAN da al’ummar Kajuru

A ɗaya ɓangaren kuma, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ta ƙaryata rahoton, da cewa babu wani abu kamar haka da ya faru a jihar.

Duk da cewa dagacin yankin ya bayyana halin da ya shiga a hannun ’yan bindigar kafin ya tsira, amma ’yan sanda da gwamnati sun ƙaryata labarin da cewa kasa kawo sunan ko mutum ɗaya daga cikin mutane kimanin 160 da Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da al’umma suka ce an sace a coci a ƙauyen.

A cewar CAN da shugabannin al’umma, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe a Cocin ECWA da Seraphim–Cherubim. An ce wasu mutane goma sha ɗaya sun samu nasarar tserewa daga hannun masu garkuwa da su.

Al’ummar yankin sun daɗe suna fuskantar hare-hare daga ’yan bindiga da ke addabar su tun daga shekarar 2018

You may also like

Leave a Comment