Marigayin dai na aiki ne a Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce an kama ɗan sandan tun ranar 15 ga watan Disamba, 2025 bisa zargin safarar makamai ba bisa ka’ida ba.sashen rundunar rundunar ’yan sandan ko-ta-kwana ta 12 da ke Minna, babban birnin jihar.
A cewarsa, yayin bincike da kuma kirga makamai da aka gudanar ranar 16 ga Disamba, 2025 domin gano bindigogi da harsasai da suka bace, Isah ya harbi kansa a ka da bindigar pistol da ya dauka daga ofis, inda ya mutu nan take.
Abiodun ya kara da cewa an kama jami’an da aka tura domin gudanar da bincike da kirga makaman saboda sakaci, saboda sun bari wanda ake zargi ya mutu ba tare da an kammala bincike ba.
Ya ce, “Ranar 16 ga Disamba, 2025 da misalin karfe 2:30 na rana, DSP Abdullahi Isah wanda aka kama tun ranar 15 ga Disamba bisa zargin safarar makamai ba bisa ka’ida ba, an kai shi ofis dinsa domin yin kirga makamai na yau da kullum.
“Abin takaici, yayin da ake cikin aikin kirga, sai jami’in ya dauki pistol daga ofis ya harbi kansa a kai, inda ya mutu nan take.
“A halin yanzu, an kama ‘yan sanda da aka tura tare da shi domin aikin kirga da bincike saboda sakaci a bakin aiki, saboda sun bari lamarin ya faru. Bincike na ci gaba,” in ji Abiodun.