Cikin wani faifan bidiyo, Bello Turji ya musanta ikirarin cewa ya karɓi kuɗi daga Bello Matawalle sai dai ya amsa cewa ya taɓa haɗuwa da gwamnan a wancan lokaci a fadar gwamnati yayin tattaunawar zaman lafiya.
A cikin wata hira da aka yi dashi, Matawalle ya amince cewa an aikawa yan bindiga wasu abubuwa amma a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma ne.
Waɗannan maganganu dai sun tayar da ƙura a Najeriya saboda yadda wasu ke zargin tsohon gwamnan na Zamfara da hannu wajen marawa ƴanbindiga baya amma a tattaunawar da suka yi a kafan yaɗa labarai ta intanet ta DCL Hausa, ya musanta waɗannan zarge-zarge.
“Shi zargi wanda ba a tabbatar da shi a kotu ba ba zama gaskiya ba, duk wani me zargi na ya je kotu, amma da sharaɗi, idan aka tabbatar da duk abin da ya fadi ba gaskiya bane a kai, toh duk abin da na aza mai na damaiji dole sai ya biya,> in the ƙaramin ministan.
Matawalle ya ƙara da cewa “Waɗannan kawai zarge-zarge ce na ƴan siyasa saboda su sa min wani baƙin jini saboda suna ganin zan koma nayi takarar gwamna.”
Matawalle ya kuma yi zargin cewa gwamnan Zamfara na yanzu na iya amfani da irin waɗannan zarge-zarge domin samun nasara a siyasa.
“Ko shi gwamnan da ya gaje ni yana ganin sai yayi haka yake samun nasara, yana ganin sai ya ɓata min suna zai iya komawa gwamna.” Matawalle ya ƙara da cewa.
Toh sai dai, babban mai taimakawa gwamnan jihar Zamfara a kan harkokin yaɗa labarai, Mustapha Jafaru Kaura ya ce zargin da Matawalle ya yi wa gwamna Dauda Lawal ba gaskiya bane.